Fasali Na Biyu
Kebance-Kebancen Fahimtar MahdawiyyanciA
Wajen Ahlulbait (a.s)
Bayan tabbatar da inganci fassarar akida kan fahimtar mahdawiyanci a wajen Ahlulbaiti (a.s) zamu shiga wani sabon fage na bincike kan wannan mafhumin, mu kuma tabbatar da cewa wadannan kebance-kebancen tabbatattu ne sun faru a cikin tarihi, kuma suna da samuwa a shari’a, kuma yarda da su (wandannan kebance-kebancen) ba ya taba akida kuma be saba da abin da ya faru a tarihi ba, wadanda su ne kamar haka:-
Kebance-Kabence Na Farko: Tabbatar Haihuwar Imam Mahdi A Wani Boyayyen Yanayi Na Musamman Da Babu Makawa Sai Ya Faru
Tare da tabbatar mahangar mahdawiyyanci a wajen Ahlulbaiti (a.s), hakika lamarin ya yawi gari a sariri cewa daga cikin mafi bayyanar wannan fahimtar, kasancewar haihuwar Imami na goma sha biyu ta faru tare da asirtawa da boyewa (a boye) don ya sami damar fakuwa bayan hakan, ya buya daga idanuwan mutane zuwa amintaccen wajen da Allah Ta'ala ya zaba masa har zuwa lokacin da zai yi masa izini da bayyana, la’akari da cewa shi ne tauraro na karshe a cikin sararin samaniyar imamanci kuma shi ne imamin da musulmai ba su da wani Imami bayansa, kuma wannan ma’anar na lazimta masa ya yi rayuwa a boye da tsawon kwana da haihuwa a boye, domin kujerar imamanci ta ci gaba da aikinta tsawon zamani ta hanyar wanzar da samuwar Imami daga cikin Imamai goma shi biyu (a.s) ya zama ga shi rayayye kuma a fake.
A wannan lokacin be dace ba wani yace
: saboda me haihuwar Imam da kuma samuwar sa bayan wafatin babansa, ba su zama abin da kowa ya gani ya sani ba, ta yadda ya zama lamarin da duk wanda yake so zai iya kai wa zuwa gare shi, don mu iya gasgata hakan ba? Tabbas da zai zama kamar haka da be sami damar fakuwa da boyuwa daga idanun mautane ba, kuma da be zama shi ne Imami na goma sha biyu ba, kuma da adadin Imamai ya fi haka, kuma hakan ya sabawa dalilan da suka zo a hadisai Annabi Muhammadu (s.a.w) a baya, hakika boyayyayiyar haihuwa na daga cikin abin da dabi’a take hukuntawa la’akari da wadannan dalilan (na hadisi).
Wannan kuwana
karafa cewa tabbatar da wani abu a fili wanda ya yi kama da lamarin haihuwan Imam Mahdi da samuwarsa da rayuwarsa (a.s) na daga cikin abin da ba zai yu yi a dogara da binciken tarihi a kan sa ba, mutukar mun sani tun farko cewa lamari ne da aka gwama shi da tsanannin asirtawa da boyewa. Ballatana ma lamari ne da ya tabbata ta bangaren akida da tarihi, wanda akida ce za ta taka rawar ta asasi a cikinsa, a daidai lokacin da binciken tarihi zai taka rawa a cikin kammaluwarsa (shi lamarin akidar), domin tun farko muna da yakini akwai wadanda suke yin inkarinta da wandanda suke yin shakku a cikinta, mutukar dai zata kasance asirtaccen lamari wanda ake boyewa, kuma wadanda ke da masaniya a kan sa wasu mutane ne ‘yan kadan, ta yadda ba za a bari wasu su sani ba koda kuwa sun kasance daga cikin na kusa da Imam (a.s), kuma ba mamaki ya zama wasu daga cikin masu ikhlasi daga ‘yan shi’a su ma su yi inkari da kokwanton haihuwarsa mutukar akwai shamaki tsakaninsu da hakinin lamarin da yake a asirce a boye, ta yanda da za a tambaye su kan haihuwar Imam Mahdi (a.s) da samuwarsa da rayuwarsa da sun musanta hakan kuma da sun gaya wa mutane cewa suma ba su gan shi ba, kuma ba su ji labarin haihuwar sa ba ko samuwarsa. Hakika mu, ba muna magana kan lamarin da ke da samuwa da jiki a sarari ta kowane bangare da fuskoki, wanda yake karkashin alkalamin tarihi dari bisa dari ba ne, ballantana mu dogara da shi (tarihi) wajen tabbatar da shi (lamarin haihuwar Imam Mahdi (a.s)) ba, ko kuma mu musa shi a bisa dogaro da maganar maruwaita da malaman tarihi ba, kadai dai muna magana ne kan lamarin da asasinsa lamarin ne na gaibu (wato boyayyen abu na akida) illa iyaka dai ba lamarin gaibu ba ne saki ba kaidi, sai cewa shi wannan lamarin yana da wani hasken da wasu zababbu ne suke kaiwa zuwa gare shi, sun san cewa an haife shi sai su bada sheda a kanta, sun san cewa ya yi gajeriyar fakewa sai su yi sheda a kanta kuma sun san cewa ya yi doguwar fakewa sai su bada sheda a kanta. Don haka ne ma mukace
hakika fahimtar Ahlulbaiti (a.s) kan mahadaawiyyanci fahimta ce ta akida.
Da ma’anar cewa inkarin masu musantawa a cikin lamari irin na samuwar Imam Mahdi, tarihi ba zai taba zama dalilin da za a iya kore samuwar sa da shi ba, tun dama tun a farko mun bayyana cewa lamarinsa asirtaccen boyayyen lamari ne. Kuma ta bangaren binciken tarihi ya zama dole mu tabbatar da samuwar wanda ya gan shi ta hanyar isuwa da labarin wanda ya ce ya gan shi ya sami tsinkayi a kansa kuma ya ji labarin samuwarsa kuma ya yi yakini da hakan, ba tare da waiwayawa ga zuwa inkarin masu inkari ba wadanda suke daukar zahiri a matsayin ma’aunin tantance asirtaccen boyayyen lamari.
Anan
zamu yi bincike guda biyu: Bahasi na farko kan dalilai da shedun da ke tabbatar da haihuwar Imam (a.s) da kuma ci gaban samuwasa, a bincike na biyu kuma zamu tattauna dalilan masu inkarin samuwarsa (a.s).
Shedu Na Tarihi Da Ke Nuni Kan Samuwar Imam Mahdi (a.s)
Wannan wani bangare ne mai fadin gaskewanda
maganganu masu yawa, na adadi mai yawa na masana tarihi suka zo a kansa, kuma zamu kasa su zuwa wasu adadi kamar haka:-
Shedar Imam Hasan Askari (a.s)kan
haihuwar dansa Imam Mahdi (a.s).
A cikin hadisai masu yawa da managartan malaman hadisai da masu ruwayana
Mazhabar Shi’a suka rawaito, wanda daga cikin su akwai:-
Hadisin da aka rawaito daga Muhammad dan Yahaya, daga Ahmad dan Ishak daga baban Hisham, Baja’fare, yace
“na ce da baban Abdullahi kwarjinika na hana ni in yi maka tambaya, shin ka yi mini izini? Sai yace
yi tanbayarka. Saina
ce: sai na ce ya shugabana shin kana da da? Sai yace
e”.
A cikin wannan hadisin akwai isuwa kan sanadinsa da manuniyarsa, ga ma litattafan mazaje (rijal) na bada sheda kan girman matsayin Muhammad dan Yahya dan Ja'afar Addar mutumin Kum, wanda kabarin sa be gushe ba sananne shahararre kuma Ahmad dan Ishak dan Abdullahi dan Sa’ad dan Akhwas Ba’ash’are dan abu Ali bakumme, ya bada sheda kan girman katsayinsa a wajen Imam Hasan Askari, (a.s).hakama
Dawud dan Kasim dan Ishak dan Abdullahi dan Ja'afar dan Abidalib baban Hashin Baja’afare shi ma ya bada sheda kan grman matsayinsa.....sannan
ka duba karancin wasidodin da ke cikin isnadin wannan hadisin wanda irinsa ana kiran sa da makusancin isnadi (mai isnadi makusanci) wanda ake ganin hakan na daga cikin abin da ke kara wa hadisin karfi.
Shedar Unguwar-zoma
wacce ita ‘yar’uwar Imami ce kuma goggo Imami, kuma diyar imami, Ba’alawiyya tsarkakakka Hakima ‘yar Muhammad Jawad kuma ‘yar ‘uwar Imam Hadi kuma goggon Imam Askari, a yayin da ta bayyana cewa ta halarci haihuwar Imamul hujja (a.s) a daren haihuwar sa,
kuma ita ce ta jibinci al’amarin - (ta kula da ita, wato ta yi wa mahaifiyar Imam Mahdi (a.s) unguwar zonci) - Narjis mahaifiyar Imamul Hujja (a.s) da izinin mahaifinsa Imam Hasan Askari (a.s).
Gomomin shedu ta hanyar ruwaya daga Imam (a.s)
Tabbas akwai jerin sunaye masu yawa na wadanda suka ga Imam Mahdi (a.s) kuma suka sami saduwa da shi kuma suka bada sheda kan cewa sun gan shi da idanunsu, wanda litattafan tarihi suka rubuta hakan, kuma wasu daga cikin marubuta suka tattarasu, a cikin litattafai na musannan misalin littafin: (tabsiratul wali fi man ra’al Ka’imul Mahdi) (a.s) na Sayyid Hashim Baharani, a cikin litattafin ya ambaci mutum (79) wadanda suka yi sheda kan cewa sun ga Imam (a.s) a lokacin yaraontarsa ko lokacin gaibar sa (fakewarsa) karama, kuma ya ambaci sunayen litattafan da ya dogara da su a kan haka. Kuma Shekh Abudalib Tajlil Al-tabrizi ya lissafo mutum (304) daga cikin wadanda suka ga Imam (a.s) kuma suka ba da shedakan
haka.
shi kuma Shekh Saduk wanda ya rasu a shekara ta (381bh) shi ma ya lissafo mutun (64) da suka tabbatar masu sun ga imam (a.s) ya ce wandannan mutanen sun bada sheda kan cewa sun ga Imam (a.s) kuma da yawa daga cikinsu ma sun kasance daga cikin wakilansa,
wadanda ke zaune a garuruwa mabanbanta.
Daga cikin wakilansa akwai: daga Azarbijan: Akwai Kasim. Daga Ahwaz: kuma akwai Muhammad dan Ibrahim dan Mihziyar daga Bagdad: Akwai Hajiz Bilali.Da Usman dan Sa’idul Amri, da Muhammad dan Usman, dan Sa’idul Amri da Ada’u.
Daga kufa kuma akwai Al’asumi, daga Kum akwai Ahmad dan Ishak.
Daga Nishabur akwaiMuhammad dan
Shazana, daga Hamadan akwai Basami da Muhammad dan Abi Abdullahil Kufi Al-asadi, da Muhammad dan Salihu.
Amma wadanda suka gan shi daga cikin wadanda ba wakilai ba ne, daga cikin su akwai mutanen Isfahan: akwai Ibin- Basha Shazale daga Ahwaz: akwai Husaini daga Bagdad akwai: Ahmad dan Hasan da Ishak Marubuci daga Banu Naubakht, da Abu Abdulllahil Khubairi, da Abu Abdullahi dan Farakh, da Abu Abdullahil kindi, da Abu Kasim bin Abi khulaisi, da Abu Kasim dan Dubaisu, da Masrurur Al-dabbakh, bawan abin Hasan (a.s), da Nabili, da Harunal Fazari. Daga Dainawar kuma akwai, Ahmad dan Abinl Hasan dan Haruna, da Ammainsa Hasan dan Haruna, daMuhammad dan
Muhammad Al-kulaini. Daga Kazwain kuma akwai Ali dan Ahmad da Muradas, daga Kum kuma akwai Hasan dan Nadhir da Husain dan Yakub da Ali dan Muhammad dan Ishak dan Muhammad dan Ishak, daMuhammad dan
Muhammad daga Misra kuma akwai abu raja. Daga Nasibaini kuma akwai abuMuhammad bin
Wajna’u Annasibi.Daga Hamadana kuma akwai Ja'afar dan Hamdan da Muhammad dan Kishmurdu, da Muhammad dan Haruna.
Daga Yeman kuma akwai Ibnil A’ajami, da Ja’afari da Hasan dan Fadhl dan Yazidu, da Abul Fadhl dan Yazid, da babansa Al-fadhlu bin Yazid da Shamshadi, kamar yanda ya ambaci wadanda suka gan shi daga mutanen Shahrruz da Saimara da Faris da Kabis da Marwa.
Shin hankali zai karbi cewa wadannan mutanen bakidayan
su, su hadu a kan su yi karya?Alhali kuma daga cikin su akwai managarta, amintattau wadanda litattafan mazaje sun bayyana nagartarsu.
Matakin da masarautar Abbasiyya ta daukakan
lamarin
Hakika masarautar abbasiya bayan da Imam Hasan Al-askari ya yi wafati ta fuskanci iyalan sa da ma’amalar da ke nuna cewa suna jin tsoron wani yaro da aka haifa wanda ke da hadari wanda ya buya daga idanunta, sai ta fara bincike ta ko wace hanya da dukkan karfin ta na iko a yayin da (Sarki) Mu’tamada ba’abbase wanda ya rasu a shekara ta (270H) ya bawa yan sandansa umarnin su bincike gidan Imamaul Askari (a.s) bincike na bin kwakkwafi, kuma ya sa a binciko dansa Mahdi (a.s) kuma ya sa aka tsare kuyangun Abu Muhammad (a.s) kuma aka kama ‘ya’yansa mata tare da temakon Ja'afar makaryaci kuma a sakamakon haka wakilan Abi Muhammad (a.s) sun kwashi mummunar jarrabawa na daga kamu da daurewa da tsoratarwa da kaskantarwa da walakantarwa da kaskanci.
Dukkaninn wannan alhali Imam Mahadi (a.s) yana dan shekara biyar daga rayuwarsa, shi kuma sarki shekarun ba su sha masa kai ba, bayan ya riga ya san cewa wannan yaron shi ne imamin da zai ruguza mulkin dagutu saboda abin da ya yadu na daga hadisi, cewa imami na goma sha biyu daga Ahlulbaiti (a.s) shi ne wanda zai cika dunya da adalci kamar yanda ta cika da zalunci da danniya, sai matsayin sa kan Mahdi (a.s) ya kasance kamar matsayin fir’auna a wajen musa (a.s) wanda mahaifiyar sa ta wurgar da shi - saboda jin tsoron - cikin korama yana dan jariri.
Mu’utamadul Abbasi ba shi kadai ne wanda ya san da wannan tabbataccen lamarin ba, hakika sarakunan da suka gabace shi kamar Mu’utaz da Muhtadi ma sun san haka, don haka ne ma Imam Hasan Askari ya kasanace yana son kar labarin haihuwarsa ya yadu, in ba tsakanin zababbun mutane daga ‘Yan Shi’arsa da bayinsa ba.
Hakika motsin da masarauta ta yi a sarari ya nuna cewa ita da sauran mutane sun yi Idrakin cewa hadisin Jabiru dan Samarata ba zai dabbaku (aywatu) a kansu ba haka ma wadanda suka gabace su daga banu umayya, wadanda wannan hadisin zai hau kansu su kadai su ne ‘yan gidan Annabta, masaukar wahayi da abin saukarwa (a.s).
In ba haka ba to wane hadari ne ke zekewa mulkin su ta hanyar dan karaminyaron
da shekarun sa ba su wuce biyar ba, kuma ba su yarda cewa shi ne Imam Mahdi (a.s) wanda hadisai mutawatirai suka yi magana a kansa ba?! Wani marubuci yana cewa da da gaske ba a haife shi ba to meye ma’anar tsare bayi mata da kulle su da tura unguwar zomomi don su tabbatar da wacece ke da ciki a cikinsu, da kuma bibiyar su tsawon lokacin da hankali ba zai karba ba, don daya daga cikinsu ta wanzu karkashin kulawa tsawon shekara biyu! Dukkanin wannan tare da fafakar sahabban Imam Hasan Askari (a.s) da munana musu tare da yada ‘yan leken asiri don su bi diddigin labarin Mahadi (a.s) da binceke gidansa lokaci bayan lokaci?.
Kuma me ya yasa
masarauta taki gamsuwa da abin da Ja'afar ya yi da’awa na cewa dan’uwansa ya rasu be bar magaji ba.
Ashe ba za ta iya ba shi hakkinsana
gado ba, tun da kamai ya zo karshe, ba tare da wanann sakaran daukar matakin ba, wanda ke yin nuni kan firgicin ta da tsoronta daga dan Hasan Allah Ta'ala ya gaggauta bayyanarsa?!
Na’am zaa
iya cewa za a iya cewa kwadayin masarauta kan taga ta bawa ko wane ma’abocin hakki hakkinsa ne ya sa ta damu da yin bincike kan samuwar da don kar Ja'afar ya cinye gadon shi kadai bisa shedar da shi da kansa ya bayar!
Kenan sai ka ce: baya daga cikin abin da ya shifi masarautar da mulki ke hannunta a wannan lokacin ta yi ta bibiyar wannan lamarin da irin wannan yanayin da ke sa a yi shakku, balle ma abin da ya kamata halifan Abbasawa ya yi shi ne ya jingina da‘awar da Ja'afar makaryaci yake yi zuwa daya daga cikin alkalai, musammamn ma da yake lamarin na daga cikin lamarin gado wanda ko da yaushe irin hakan na faruwa sau da yawa, a wannan lokacin zai zama cewa alkali na da ikon ya kafa comitin bincike, a misali sai ya kira gwaggon Imam Hasan Askari (a.s) da mahaifiyarsa, da kuyangun Imam Hasan Askari daga banu Hashim, sannan ya saurarai maganganunusu, ya dawwana shedarsu sannan komai ya zo karshe. Amma fitar wannan lamarin daga hannun alkali tare da cewa abin da ya shafi shi ne, kari a kan matakin da azzalumar hukuma ta dauka kamar yadda bayaninsa ya gabata, dukkanin wannan na tabbatar da cewa hukuma na da tabbaci kan cewa mahadin da aka yi alkawari shi ne zurin sarka na karshe daga cikin zuriya tsarkakakka wanda ba zai taba yiyuwa sarkar ta tsinke daga kan Imami na goma sha daya Imam Askari (a.s) ba, musamman ma da yake hadisai masu yawa sun zo ta bangaren kowa inda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa: “lalle su biyun nan: ma’ana kur’ani da Ahlulbaiti (a.s) - ba za su taba rabuwa ba har sai sun iske shi a tafki”. Kuma ma’anar rashin haihuwar Imam Mahdi (a.s) ko kuma rashin wanzuwarsa a raye ita ce karewar Ahlulbaiti (a.s), kuma ba wanda ke fadin wannan daga cikin wadnda ake kira da (shuwagabannin muminai) daga Abbasawa, domin hakan karyatawa ne ga mafi girman Annanbawa, Manzonmu Muhammad (s.a.w), kai kwata-katwa ba daya daga cikin musulmai da yake fadin haka in ba wanda ya dauki karyata wannan al’amarin ba a bakin komai ba, ko wanda ya yaudari kansa a wajen yin ta’awilin hadisin nauyaya biyu ba ya karkatar da manuniyarsa zuwa ga abin tafarki mabayyani be tabbatar da shi ba.
Tabbatar da haihuwar Imam Mahdi (a.s) daga bakunan malaman Ahlussuna
Sayyid Samir Umaidi yace
a cikin wannan kan wannan lamarin:
Malaman fakihai da masana hadisi da mafassara kur’ani malaman tarihi da masu tahkiki da malaman adabi, da marubuta daga cikin Ahlussunna sun tabbatar da haihuwar Imam Mahdi (a.s) tabbatarwa mabayyaniya sama da sau dari, kuma sama da rabinsu sun bayyana cewa Imam Muhammad dan Hasan Al-Mahdi (aj) shi ne shi ne limamain da aka yi alkawarin zai bayyana a kardshen zamani.
Kuma hakikana
jeranta wadannan maganganun bisa shekarun rasuwar ma’abotan su, sai na samu cewa lokacin rayuwarsu ya hade da juna, ta yadda yin zamani daya da wanda aka gabace shi da kuma wanda ya gabata ba zai zama abu mai wahala ba. Wanna kuma tun daga zamanin gajeriyar fakuwa har zuwa wannan lokacin namu, kuma da sannu zamu ambaci maganganun da suka zo hannuna daga wasunsu daga masdarorinsu yayin da muka zo magana kanasu, tare da isuwa da ambaton sunayen wasu daga cikinsu, ba tare da fadin sunansu ba, saboda lissafosu a cikin wannan fasalin ya ci tura, ta yadda maganganunsu sun kai kimanin zantuka ishirin da tara, a cikin daya daga cikinsu (wadannan litattafan) a littafin Ilzamil Nasib ya zo cewa akwai kimanin sama da littafi dari (da aka yi magana a cikinsu kan hakan),
ya kake gani da za a ce mu jero dukkanin maganganunsu, baki dayansu? Bisa cewa abin da zamu ambata a cikin matani yake, ba tare da mun yi nuni zuwa masdarinsa ba a hamishi (ruburn kasan takarda) ba, wannan dalili ne kan cewa mun cirato shi daga cikin litattafan shi’a imamaiyya wadanda sun rigaya a wannan fagen tare da kiyayewa wajen dauwana lambar littafi da lamba shafi da waje da kuma shekarar bugawa, ta yiyu ya zama daga cikin mafi yalwatawa a cikin wannan babin littafin “Al-Mahdil Muntazar Fi Nahjul Balaga”. Na shekh Mahdi Fakih Imani, a inda ya ambaci mutum dari da biyu daga mazajen ahlussunna wadanda suka tabbatar da hakan,
yana mai isuwa da ambaton sunayensu da masdarorinsu tare da juzu’in da shafukansu ba tare da bijiro da maganganunsu ba, ta yiyu ya bukaci bayyana wassidar sa zuwa gare su cikin mutukar kiyayewa, kuma hakika kimanin sunaye talatin ne suka tsere masa, kuma shi ne babbar madogarar mu, kuma ba mu iya riskar wani abu ba, domin abin da ya tsere masa wani na ya rigaye ni zuwa gare shi, har sai da rawar da na taka a cikn wannan dalilin ta zama ita ce hadawa da jarantawa a tsawon karnoni kawai.
Sannan ya ambaci sunayen marubuta (128), daga cikin marubutan Ahlussunna da suka ambaci imama Mahdi (a.s) a matsayin imamina
goma sha biyu da ga imaman Ahlulbaiti (a.s).
Daga cikinsa
akwai wanda ya yi zamani da lokacin da aka haife shi da kuma gajeriyar fakewa kuma shedar wadannan malamai abar la’akari ce a tarihi kamar yanda aka sani, daga cikinsu akwai
Abubakar Ruyani, Muhammad dan Haruna (wanda
ya rasu a shekara ta 307 a cikin littafinsa (musnad).
Ahmad dan Ibrahim dan Ali al-kindi, daga cikin daliban ibni jariri al-dabariwanda
ya rasu a shekara ta (320BH).
Muhammad dan Ahmad dan Abis-Salji, Abubakar Albagdadi (wanda ya rasu a shekara ta 322) a cikin (Mawalidil A’imma) an buga shi tare da littafin (al- fusul Ashara fil gaiba) na shehul mufidi, tare da littafin (Nawadirul Rawandi) bugun Najaf Madaukakiya shekara ta (1370BH), daga cikin wadanda suke kusa da shi a zamani daga cikin masana akwai: Khawarizmi (wanda ya rasu shekara ta 387) a cikin (Mafatihul Ulum 32, 33) bugun London 1895M).
‘Yar Matsaya Tare Da Masu Musantawa
Ya bayyana a sarari daga abin da ya gabata cewa mas’alar mahdawiyyanci ma’ala ce ta akida tun kafin ta kasance mas’ala ta tarihi kuma dalilin da ke tabbatar da ita dalili ne na Akida kafin ya kasance dalili na tarihi, kuma ya bayyana a sarari cewa akwai tarin dalilan da suke tabbatar da ita kuma ya bayyana cewa tabbas boyayyen lamari na gaibu kamar irin na Imam Mahdi (a.s) a al’adance ya gaji fuskantar masu musanta shi, domin abin da ke boyuwa daga idanuwan mutane na da manufa daga manufofi, wanda abin da ake nufi da hakan kar wani daga cikin mutane ya gan shi ta yanda idan an tambayi mutane a kan sa zasu ce: ba mu ganshi ba, ko da kuwa suna daga cikin mafi kusancin mutane zuwa gare shi, kuma mun fadi cewa musantawar irin wadannan mutanen ga abin da yake boyayye ba zai zama ingantaccen dalili kan rashin samuwar abin ba, wannan ce mararraba ta asasi wacce masu musanta haihuwa da samuwar Imam Mahadi (a.s) suka fada ciki, domin su sun tafi suna ta binciken iran wannan nau’in madogarar a cikin tarihi, a yayain da suka kasa samun wani abu daga irinta (madogarar) sai suka dauke shi a matsayin dalili kan rashin haihuwa da samuwar Imam Mahdi (a.s), tamkar dai sabanin Shi’a kan lokacin da aka haifi Imam Mahdi (a.s) da sunansa da shaidar Ja'afar makaryaci baffan Imam Mahdi (a.s) ta cewa dan’uwansa ya rasu be bar magaji ba.
Kuma asasin tattaunawar mu tare da wadannan shi ne cewa hakika tafarkin nan na tarihi za a iya yin hukunci da shi kan mas’alolin da ake iya riska (da hawas guda biyar) wadanda tun daga farkon su har karshe sun faru ne a idon muruwaita da marubuta tarihi misalin waki’ar siffin da waki’ar karbala.....da sauransa, kuma ba daidai ba ne a hukunta mas’alolin gaibu na akida da wannan ma’aunin (na ruwayar tarihi) kan asalin samuwarsu ba,
kuma wannan lamarin na da hasken da ake iya riska a wajen zababbabun mutane ta yadda, da za a tambayi mutane game gari kan wannan lamarin da sun musanta shi. To ta yaya kuma zamu dauki musanatawar game gari daga mutane a matsayin dalilikan
rashin samuwar wani lamarin da masu shi tun tuni suka yi imani da cewa ba abu ne da za a iya gani ba, in ba ga daidaikun zababbaun mutane ba?
Hakika abin da ya kamata ga wanda yake so ya yi jayyaya kan mas’alar Imam Mahdi (a.s) ya fara ne tun daga tushen mas’alar ta akida ba ya dauke ta daga wani yankin ta da ya danganci tarihi ba, domin lamari ne da ya zama, da gangan ake so ya zama boyayye a asirce daga idanuwan mutane mafiya kusanci, ta yadda da ba za a rasa samun sabani a kan wasu bangarorin lamarin ba, na daga irin sabani da aka samu kan lokacin haihuwar Imam da sabani kan sunan mahiafiyarsa, kuma sheda irin shedar Ja’afar makaryaci ba zata cutar ba, domin a dabi’anci amsar da za a bayar a irin wannan yanayin ita ce: hakika sabanin kan shekarar haihuwa da sunan mahaifiya, wannan abu ne na dabi’a a sarari sakamomakon dagewar Imam Hasan Al-askari kan boye yadda lamarin yake dalla-dalla cikakkiyar buyewa daga idanun mafiya kusanci makusanta, Don toshe kafar isar labarin zuwa mahukunta Abbasawa, kamar yadda shedar da Ja'afar makaryaci ya bayar kan cewa dan’uwansa ya rasu be bar baya ba (wato be bar da ko ‘ya ba), ta faru ne sakamakun haka, ta yadda Imam Hasan Al’askari ya so ya boye haihuwar dan’sa ga dan’uwansa, sai Al’amarin ya zama a wajensa kai ka ce Imam ba shi da magaji a baynasa kuma wannan matakin da Imam ya dauka a kan dan’uwansa ya yi daidai da hankali ko da kuwa dan’uwan na sa be zama makaryaci da aka yi masa sheda da fasikanci ba, ta yaya kuwa!, ballantana ma an shedi Ja'afar makaryaci da yin haka.